30 Nuwamba 2021 - 11:56
​Batun Cire Takunkumi Ne Kan Gaba A Tattaunawar Da Ake yi Kan Shirin Nukiliyar Iran A Biyanna

Rahotanni sun bayyana cewa tuni aka fara sabuwar tattaunawa kan shirin nukiliyar iran a matakin mataimakan ministocin harkokin waje da Darektoci na iran da na sauran abokan tattaunawar, wanda Ali Bagheri Kani babban Jami’in kasar Iran a tattaunawar yake jagoranta, kuma tawagar Iran ta bayyana batun cire mata takunkumi a matsayin Jigon tattaunawar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Bayan kwashe shekaru 13 ana kai ruwa rana game da shirin nukiliyar na kasar Iran daga karshen an cimma matsaya a shekara ta 2015 makon guda bayan nan kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya fitar da kuduri mai lamba 2231 na goyon bayan yarjejeniya wacce ake kira JCPOA a takaice.

Sai dai tsohon shugaban Amurka Donald Trumph na hawa mulki a cikin watan Mayu na shekara ta 2018 ya fice daga yarjejeniyar, kana ya kakabawa kasar ta Iran sabbin takunkuman tattalin arziki mafi tsauri a tarihi kan kasar, da kuma karin matsin lamba a kanta.

Sai dai Iran ta dauke matakin jingine yin aiki da wasu yarjeniyoyin da aka cimma domin mayar da martani kan takunkumin. Har’ila yau ta jaddada cewa matukar sauran abokan tattaunawarta za su yi aiki da alkawuran da suka dauka to ita ma Iran za ta dawo da yin aiki da bangarorin da ta jingi ne.

342/